Tuesday, August 14, 2012

ALI SALISU ALISTO

ALI SALISU AISTO JARUMI MAI YAYI Jarumin dan asalin garin maradi a jamhoriyar niger, ya dage wajan ganin ya ciri tuta a harkar wasan hausa a niger dan ya taka muhimmiyar rawa a fina finai kamar su jagwal da ummaru. sannan kuma jarumin yana daya daga cikin maaikatan radio garkuwa a maradi, yana isar da gaisuwarsa ga masoyansa

BINIYA TAKO TAKO

BINIYA TAKO TAKO ZINARIN ZAMANI A wannan zamani da duniya take bukatar masu fasaha da hikima da kwarewar aiki tare da bada himma akan alamuran yauda da kullun, daya daga cikin jaruman da suka dage akan cigaban adabi ta hanyar shirya finafinai na hausa musamman na kasar niger dan fadakarwa da ilimantarwa, wato BINIYAMINU UMMAR TAKO. Dan asalin jahar maradi ta jamhuriyar niger, jarumin yana mika gaisuwar sa ga dukkanin ilahirin masoyansa, sannan jarumin ya tagoranci finafinai da dama. kamar su Jagwal, Ajalinka, Ummaru
+22796721606, +22794137830

Friday, November 18, 2011

ALLAH YAYI WA MUSTAFA B. MOHD RASUWA

MUSTAFA B.MOHD


Inna rillahi wainn ilaihi raju'un Allah yayiwa daya dagacikin manyan Directocin hausa film na birnin katsian rasuwa, kafin rasuwarsa ya kasance daya daga cikin masubada umarni a hausa film kuma jigo a kungiyar wasan hausa ta jihar katsina,chairman na kungiyar Directoci ta MOPPAN katsian, ya bada umarni a finafinai da dadama, kamr dufana, sabati, tuntuban harshe da dai sauransu
Allah ya jikan sa ya kuma kyautata namu zuwan

Daga salisu nauku

Monday, October 17, 2011

YA 'U COMMANDER ( CONTINITY DIRECTOR )

YA'U COMMANDER
EMAIL:- yaucommander@ymail.com 08137709426
Ya'u commander yana daya daga cikin masu shirya finafinan wasan hausa a jihar katsina, kuma jijo a kungiyar wasan hausan jihar katsina,sannan kuma Director/ Continity Director. Ya shirya fina finan dadama, kuma ya bada gudunmuwa a fianafinai da dama kamar:- NASARUN MUNALLAH, BABBAN ZANCE, SANADIYYA, BABBAN LABARI, wakilin taurari Salisu Abubabakr nauku ya zanta dashi inda yabada tarihin rayuwarsa.

Taurari Ko malam ya u commander ko zaka iya bayyayana mana sunan ka?

Ya'u commander- Yayi murmushi yace to nidai sunana ARMA YA'UA MAMMAM kuma dan asalin jihar katsina, an kuma haifeni a birnin katinan dokku, sannan ina alfahari da garina

Taurari:- ko zaka iya fadawa mana dalilin dayasa ka tsince kanka cikin wanana san'a

Ya'u commander:- To ni dai tun ina karami maabocin shaawar kallon fina finai ne, bayan kuma na girma nayi wayo sai na ji ina shaawar kare kimar yarena da aladata, wannan ne yasa na tsinci kaina ina shaawar shiga harkar wasan hausa, wanda daga bisani na shiga wata kungiya anan garin katsina mai suna katianawa film production, daga nan muka cigaba da fsdi tashi na kai ga nashiga cikin jagororin kungiyar, domin na rike mukanin sakatare a kungiyar.

Taurar:- to malam ya'u ya batun ilmi kuma, jama'a zasu so ji irin gwagwamayar da aka sha akan neman ilimi.

Ya'u commander:- to dai kamar yadda kasani cewa neman ilimi wani abu ne mai bukatar hakuri da ja jir cewa, gaskiya ne domin kuwa na yi ilimi na addini dana zamani, donim nayi makarantar islamiyya na kuma yi primary school a Dotsin Amare primary school,na kuma yi secondary school dina a Katsina collage Katsina, kuam har yanzo ina bada ilimi.

Taurari:- To commander a wani film ka fara aiki? kuma a wani kamfani?
Ya'u commander:-Gaskiya ne nafara aikin fim dina akungiyar dana fara shiga watu katsinawa, kuma sunan nan fin din Abinda rai keso

Taurari:- to malam ya'u kagaya man fina finan da kayi aiki acikin so

Yau' commander:- Nayi aiki a finafinai dayawa irn su SANADYYA, KAIDAI KAGA MUTUN, DAN AUTA A NAGO, NASARUNMALLAH, DAN AUTA DA KANDE, BABBAN ZANCE, BABBAN LABARI, TSINAKAYE, SANANIN FULANI, GOBAR RAYUWA, DAFIN ZUCIYA, DA SAURANSU.
Taurari:- To malan ya'u commander mun gode
Ya'u commamder:- Nima nagode

Saturday, September 17, 2011

AJALINKA............

AJALINKA Labarin ne akan wani mutun da shiryawa matar sa balagoran karya dan ya cinmma burinsa bisa bukatarsa tayin badala agidansa, amma kuma bayan tafiyar matar tasa sai ludayin ya juya da wani yanayi a gareshi, domin tsoran da ka ringa bashi a ckin gidan da firgitarwa, wanda hakan yayi sanadiyyar rashin biyan bukatar sa har matar sa ta dawo. Duk da cewa ya kira kansa soja, tare da yiwa yarinyar daya dauko karyar ya halacci yakeyake kala kala.
PRODUCER DIRECTOR Faruk isa Bassiru garba +22794327030, +22796721606 +22797815417

JAGWAL

KUDIRI MARADAWA PRODUCTION
KE GABATAR DA
JAGWAL
A wannnan karin Maradawa wato yan Niger sun zage dantse, inda suka yunkura suka fito da wani sabon film mai suna jagwal , wanda ya kunshi labari mai ilimantrarwa da fadakarwa da nishadantarwa akan rayuwa.
JAGWAL Labarin wasu mutanene da suka yi masayan jarirai, karancewar daya maikudi ne ya sa ya sayi jaririn talakan akan makudan kudade kawai dan san da namiji, ya kuma bi bayansa yashi yasa aka kashi shida iyalansa domin ganin bukatarsa ta biya.
Amma ina daga bisani bayan wasu shekaru sai wata sabuwa ta bullu, ta zowa Alhajin da wata kala.
Domin ganin yadda ta kasance sai kanemi film din JAGWAL

WASO DAGA CIKIN JARUMAN FILM JAGWAL

RAIYA

FARUKU ISA

ABUBKAR MURFI


NAFISA ABUBAKAR


RASHIDA

Tuesday, April 19, 2011

SALISU ABUBAKAR NAUKU( EDITOR)

DAGA EDITAN TAURARI
SALISU NAUKU
Ina yiwa yan'uwa da abokan arziki fatan alheri musamman masu ziyarar wannan shafi namu, wanda yake magana akan adabin hausa da kuma wasan hausa, saboda haka ne nakewa maabota shiga wannan shafi albishir da cewa, duk wani dan wasan hausa yana da damar zai iya bada cikakken tarihinsa, kuma mujallar taurari zata sa tarihin nasa
domin neman karin bayani sai a nememu akan wannan lambar 08135414888,07092405373 ko taurari@gmail.com