Monday, October 17, 2011

YA 'U COMMANDER ( CONTINITY DIRECTOR )

YA'U COMMANDER
EMAIL:- yaucommander@ymail.com 08137709426
Ya'u commander yana daya daga cikin masu shirya finafinan wasan hausa a jihar katsina, kuma jijo a kungiyar wasan hausan jihar katsina,sannan kuma Director/ Continity Director. Ya shirya fina finan dadama, kuma ya bada gudunmuwa a fianafinai da dama kamar:- NASARUN MUNALLAH, BABBAN ZANCE, SANADIYYA, BABBAN LABARI, wakilin taurari Salisu Abubabakr nauku ya zanta dashi inda yabada tarihin rayuwarsa.

Taurari Ko malam ya u commander ko zaka iya bayyayana mana sunan ka?

Ya'u commander- Yayi murmushi yace to nidai sunana ARMA YA'UA MAMMAM kuma dan asalin jihar katsina, an kuma haifeni a birnin katinan dokku, sannan ina alfahari da garina

Taurari:- ko zaka iya fadawa mana dalilin dayasa ka tsince kanka cikin wanana san'a

Ya'u commander:- To ni dai tun ina karami maabocin shaawar kallon fina finai ne, bayan kuma na girma nayi wayo sai na ji ina shaawar kare kimar yarena da aladata, wannan ne yasa na tsinci kaina ina shaawar shiga harkar wasan hausa, wanda daga bisani na shiga wata kungiya anan garin katsina mai suna katianawa film production, daga nan muka cigaba da fsdi tashi na kai ga nashiga cikin jagororin kungiyar, domin na rike mukanin sakatare a kungiyar.

Taurar:- to malam ya'u ya batun ilmi kuma, jama'a zasu so ji irin gwagwamayar da aka sha akan neman ilimi.

Ya'u commander:- to dai kamar yadda kasani cewa neman ilimi wani abu ne mai bukatar hakuri da ja jir cewa, gaskiya ne domin kuwa na yi ilimi na addini dana zamani, donim nayi makarantar islamiyya na kuma yi primary school a Dotsin Amare primary school,na kuma yi secondary school dina a Katsina collage Katsina, kuam har yanzo ina bada ilimi.

Taurari:- To commander a wani film ka fara aiki? kuma a wani kamfani?
Ya'u commander:-Gaskiya ne nafara aikin fim dina akungiyar dana fara shiga watu katsinawa, kuma sunan nan fin din Abinda rai keso

Taurari:- to malam ya'u kagaya man fina finan da kayi aiki acikin so

Yau' commander:- Nayi aiki a finafinai dayawa irn su SANADYYA, KAIDAI KAGA MUTUN, DAN AUTA A NAGO, NASARUNMALLAH, DAN AUTA DA KANDE, BABBAN ZANCE, BABBAN LABARI, TSINAKAYE, SANANIN FULANI, GOBAR RAYUWA, DAFIN ZUCIYA, DA SAURANSU.
Taurari:- To malan ya'u commander mun gode
Ya'u commamder:- Nima nagode