Thursday, November 25, 2010

ABDU BODA

TARE DA SALISU NAUKU
ABDU BODA YA KARBO AWARD A KASAR SUDAN

wasan hausa yana daya daga cikn manyan adabin dake nuna al'adun bahaushe, harma in an tashi duba madubin daza aleko al'adun bahaushen akanyi anfani da wasan hausan, wanda hakan yayi sanadiyyar gayyatar jaruman da suka ciri tuta a fannika da dama kamar su fitowa acikin film, mawaka,directoci, da sauran masu ruwa datsaki a harkar,domin karbo lambobin girmamawa, da sauran abubuwan da suka shafi harkar.
An gayyaci manyan jarumai zuwa kasashe daban daban, kamarsu Ali, Sani Danja, da sauransu kuma sun karbi lambobin girmamawa daban daban, daga kasashe dadama

Kasar Sudan tana daya daga cikin kasashen da hausawa sukayi yawa sosai, kuma itace kasar da sukayi kamanceceniya sosai a wajan al'adu da kasar hausa, domin kuwa tarihi ya nuna cewa al'adun kasar hausan ansamosune daga kasar larabawa, kuma sun fitone dagan Sudan din.

kasar sudan ta kan shirya wasanni na al'adu, da kuma ba jarumai lamboobin girmamawa, garmamawa daban daban, a wannan karamma sun shiya wasanni irin wadanda suka saba, wanda suka gayyaci mutun daya daga Nigeria domin su girmamashi saboda gwanintarsa a bangarori da dama kamarsu, Waka, Fitowa cikin film, da kuma daukar nauyi shirya film dain hausa Wato ABDU BODA KATSINA.
A cewarsa Jarumin wannan yana daya daga cikin abubuwan da bazai mantasu a ayuwarsaba, domin burin kowanne jarumi yaga ya mallaki lambar girmamawa domin hakan zai kara masa karfin gwuiwa nacigaba da harkokin.
Daga basini kuma yayiwa Allah godiya, da kuma yiwa masoyansa fatan alkhairi.
ZAKU IYA SAMUNSA A WEBSIDE www.abudoda.blogspot.com
wasu daga finafinansa Jarumin yayi finafinai masu ilimantarwa,fadakarwa, da nishadantarwa, kamarsu DUNIYA,BABBAR KASUWA, BABBAN TARO, DABAYBAYI, BABAKERE, KAUSAR, YAHABIYA, MATAR MUTUN, SANSANIN FULANI,