Friday, January 8, 2010

TARE DA SALISU ABUBAKAR NA UKU
TARIHIN ALI NUHU
TAURARON WASAN HAUSAALI HUNU
Ra’ayi muna son Ali Nuhu ya bayyana mana takaitacen tarihin rayuwarsa ?
Ali Nuhu : Ni dai dan Najeriya ne, an haife ni a shekarar alif dari tara da saba’in da hudu(1974) a jahar Barno cikin garin Meduguri, daga nan na girma a cikin jahar Kano inda a nan na yi karatuna na pramare da sakandre, daga bisani na karasa a university ta garin Jos, sai na tafi bautar kasa a Ibadan, daga nan na dawo jahar Kano inda na fara shirya fina-finan Hausa.


Ra’ayi : miye yaja ra’ayin ka har ka shiga shirya fina-finan Hausar ?

Ali Nuhu : To’ ni dai tun ina karami ina kallon fina-finai irin na Indiya, da na turawa, tare da kallon wasannin kwaikwayo na hausa irin na su Kasimu Yaro da dai sauransu, da yake nima ina da ra’ayin in na girma in dinga yin irin wannan wasa, sai gashi kuma bayan na girman Allah ya cika mani burina na fara yi.


Ra’ayi : ko wace irin sana’a da farko bata rasa wahalhalu kafin a cimma ribarta, ko zaka iya fada mana wahalhalun da ka sha karo da su, kafin ka kai ga wannan matsayi da kake a halin yanzu ?

Ali Nuhu : E’ to gaskiya ba a rasa wahalhalu a kowace irin sana’a, wahala ta farko da na fara fuskanta ita ce, lokacin da ina sabon shiga akasari mu sabin yan wasa mu kan bi kofa-kofar kampanonin shirya fina-finai da sunan ziyara, ko hira, domin dai kar a manta ka.Abu na biyu kuma dazan iya cewa mai wahala shine, lokacin kasan babu wayar Salula balantana in ana neman ka nan take a yi amfani da ita a san inda kake, dan haka da an neme ka domin ka taka wani Sin ba a same ka ba to shi kenan, ana ganin wani sai ayi amfani dashi.

Irin wadannan matsaloli sune zan iya cewa matsalolin da na dan fuskanta a farkon shigata harkar fim.Amma a halin yanzu sai dai mu ce mun godewa Allah, mun godewa manyan mu da muka samu a cikin wannan haraka, domin basu nuna mana bakin-ciki ko kyashi ba, sun nuna yakamata muma mu shigo a yi damu kuma Alhamdu Lillahi an samu biya bukata, gashi kuma har Allah ya kawo mu wannan matsayi. Ra’ayi : masana yare da al’adun hausa na ganin fina-finan da kuke yi basu da alaka da al’adun hausawa, balantana su ciyar da yaren ko al’adun hausar gaba, ganin irin yadda ku ka cakuda al’adun turawa da na indiya a cikin na hausa ko mi zaka ce anan ?

Ali Nuhu : To ni a kulum irin wadannan mutane abinda na ke nuna musu shi ne, in a kace al’ada ana nufin yanayin zamantakewa da kuma rayuwa mutum ta yau da kulum, to in kace an kaucewa tsarin al’ada ta bahaushe, sai a tambayeka minene aka yi wanda ya kaucewa al’adar bahaushe. Na san dai watakila suce rawa da waka da ake yi, to bahaushe dai yana rawa da waka ba tun yanzu ba tun a da can baya, abinda kawai mutum zaice shine, tsarin yadda ake rawa da waka a da ba irin na yanzu bane, domin komai yanzu an riga an sa cigaba a cikinsa, ko a makarantar Allo inka ka dauka a da a fili ake tara almajirai a hada itace a kunna wuta su kewaya suna karatu.

Yanzu kuma ka gani a cikin Aji ake koyar da su, a kan tebura da kujeru ko ba haka ba ? ka gani kenan al’adar ta canja bisa yadda ake yinta a da, to haka ne canjin yanayin rayuwa aka samu a ko ina. Wani misali in ka dauki bahaushen mutum a zamanin yanzu musamman matashi, kashi 90 cikin 100 zaka ga yana sanye ne da wandon Jins da dai sauran sutura irin na turawa, to kaga yanayin al’adar bahaushe kenan ta yanzu, amma kuma a da can baya ba haka yanayin al’adar bahaushe take ba. Ni da dai irin wadannan mutane za su rika cewa ne, a rinka tuno da al’adunmu na hausa na can baya dan kar su gushe harma a manta da su, wannan bai zama laifi ba, amma ba wai suce an kaucewa al’ada ba, yadda rayuwarka take ai shine al’adarka.


Ra’ayi : Dan mi a cikin fina-finanku ku ka fi kwaikwayon fina-finan Indiya da na Amerika ?

Ali Nuhu : Yanzu ka dauka kasashe irin su Najeriya da Nijar duk ba siyasa ake ba ? siyasar da ake yi ba irin ta turawa bace suka kwaikwaya suna yi ba ? mi yasa baza a kirkiro da wata siyasa ba a ce gata siyasa ce irin ta yan Nijar ko yan Najeriya mu daina amfani da irinta turawa, amma ka gani ba a yi ba sai irin tasu din dai muke yi.

Ai komi da ke faruwa yanzu a duniya an riga an ayyana a rai, turawa su suka cigaba saboda haka komi da ake kokarin yi ana kokarin yin irin nasu ne,kai bamu hausawa ba ma, ka dauka balarabe da yake da akida da ra’ayi kan al’adunsa da addinin sa kwaikwayon ba’amurke yake, shiga irin tasa da sauransu, to abu ne da zamani ya taho dashi, kuma a gaskiya a wannan lokaci da muke ciki in kana son a ce ana yi da kai doli ne ka bi wannan zamani, idan kuma ka ki to gaskiya ba za ka kai labari ba.


Ra’ayi :Ana zargin Ali Nuhu da girman kai, da kuma wulakanta mutane, mine ne gaskiyar lamarin ?

Ali Nuhu : Yayi dariya ! yace to kasan dai bahaushe yace gani ya kori ji, kuma a zahirin gaskiya ni abinda zance akan wannan shi ne, zan fi so in muka gana da mutum, sai ya yankewa kansa hukumci in yaga yanayin yadda muka yi mu’amala dashi, domin yanzu zan iya fadar abu ya kasance na fada ne dan in gyara kaina ko makamancin haka, gara dai mu hadun in muka hadu da mutum ka gani shi sai ya yankewa kansa hukumci.TAKAITACCEN TARIHIN SALISU NA UKU
Sunana Salisu Abubakar wanda akafisani da NA UKU, kuma ni dan asalin Kasar Niger ne a garin Maradi, kuma haifaffen Birnin kanon Negeria a unguwar nasarawa, ina kuma alfahari da garuruwana na asali dana haihuwa, Alhamdu lillahi na mallaki takardar shedar kammala karatun primari a (yammata primary school, Dala L. G. A.) na kuma sami ta Secondary a (kofar Ruwa Boys secondary school) daga nan na garzaya domin samun damar mallakar wata shedar karatun, inda na sami Certificate in public adminstration ma’ana mulki da al’amuran yauda kullun a (federal collage of education F.C.E. kano).
Banyi kasa a gwuiwaba na garzaya domin mallakar ilmin naora mai kwakwalwa wato Computer a (Abacom computer Academy Kano) daga nan sai na tsince kaina cike da sha’awar zurfafa ilimina akan naura mai kwakwalwa inda naci gaba da karatu a Jami’ar Bayaro, kuma nayi karatu a karkashin wata Jami’ar nan ta kasar Amurka wato (Sanfran Cisco University) na kumaci nasarar samun shedar kammala karatun ilimiin naura mai kwakwalwa mai zurfi wato (Cisco certificate C.C.N.A), bayan haka kuma na hallaci marantar karatun harkar wasan kwaikwayo a Kaduna mai suna (Dream wever) inda nayi nazari akan bada umarni, na kuma Halacci tarurruka da dama wadanda suka kamaga tarun karawa juna sani wadanda suka hada dana Yan’jarida, harkar wasan hausa, da kuma na marubuta.
Bayan na sani nasarori da dama wajan neman ilimi, na kuma tsinci kaina a ma’aikatu da dama inda nayi aiki dasu,domin samun kwarewa akan abubuwan dana karanta, inda nayi aiki da Arewa Best Academy, Center for Excellent Computer Academy, BAMI Excellent Maradi a matsayin Malamin English, daga nan kuma na shiga hudda da kamfaninnokan Jarida, gidajen Radiyoyi Kamarsu, Leadership, Radiyo Garkuwa Maradi,da Radiyo Sarauniya Maradi, da sauran kafufin yada labarai.
Daga bisani kuma na shiga harkar wasan hausa, inda nakasance marubucin Labaran finafinan hausa, na kuma fara bada umarni a wasu finafinan kamar su Tagwayen Surri, Auta Sarki da sauransu ,sannan kuma na bude kamfanina mai suna NA UKU MULTIMEDIA nakuma yi masa rijista da kungiyar ‘yan wasan hausa ta kasa data jiha wato (MOPPAN)wasu daga cikin finafinaina, Bakar tukunya, Tagwayen surri, kai dai kaga mutun, Karaga.
Sannan kuma bazan mantaba nayi farin cikin dana jagoranci Bude Mujallar internet mai suna, www.wasanhausa.8m.net, wacce take kunshe da labaran yan wasan hausa kawai, sannan kuma ina alfahari da godiya ga Allah daya bani damar Bade wannan shafi na TAURARI wanda ya kunshi bayanai akan Adabin Hausa,wasan hausa,da kuma tarihin wasu wadanda suka bayar da gudunmuwa wajan cigaban Al’umma, kama da shugabannin kungiyoyi,yan’siyasa, shugabannin masu mulki, sarakuna, da dai suaransu

1 comment:

  1. Na yi farinciki da wannan tarihi na ka da nai karo da shi a halin ina bukatar taimakon irinka kan laptop dina da na canza ma pswd ta ki buduwa da sabo ko tsohon pswd din.

    ReplyDelete