Sunday, November 15, 2009

TASKAR WASAN HAUSA

TARE DA SALISU NA UKU
ZANGO YACE BA BAKATAFE BANE, SHI BAHAUSHENE MUSULMI


BA kamar Zangon Daura ko Unguwar Zango Bare-Bari da ke cikin Jihar Kano ba, wa]anda wurare ne da suka yi suna a tarGhin }asar Hausa, Zango Kataf gari ne wanda yawancin mazaunan sa }abilar Katafawa ne. garin ya yi }aurin suna kuma ya ajiye mummunan tarihin fa]an }abilanci da na addini inda aka kashe ]aruruwan mutane. A wannan garin ne aka haifi Adamu Abdullahi, ko kuma mu ce Adam A. Zango, fitaccen jarumin nan da aka sani da la}abin ‘Usher’.

A lokacin da aka yi rikicin Zango }ataf, Adam yana yaro }arami inda yake karatu a makarantar ‘Zango 1 Primary School.’ A hirar da ya yi da wakilinmu, jarumin ya labarta mana cewa, "Lokacin da rikicin kashe-kashen Zango Kataf ya ~arke, ni ina }arami, kusan ban san komai ba. Sai ma ~oye ni da aka yi kamar yadda aka ri}a ~oye sauran yara }anana".

A nan sai Adam ya sunkuyar da kai ya tuna abin da ya gani a lokacin rikicin. "Ka san bayan an yi kwanaki ana rikici, to daga bisani ‘yan sanda sun zo suka tcsirar da mu daga harin {atafawa. To a gafen titi na ga tulin gawarwaki birjik, har da na wa]anda na sani."

Ba wannan bala’in ka]ai Adam ya gani ba. Ya }ara da cewa ya ga yadda aka ri}a banka wa gidaje wuta suna }onewa }urmus.

Adam ya }ara da cewa daga nan ne wani kawunsa mai suna Alhaji Rabo Musa Salisu ya ]auke shi tare da sauran dangi ya ranga]a da su garin Jos. Ko Adam ya san gwarzon Katafawa wanda aka yi wa shari’a bisa zargin shi ne ummulhaba’isan kisan kiyashin da aka yi, wato Janar Zamani Lekwot, ido da ido kuwa? "A’a, ni ban san shi ba, sai dai sunansa da kuma aika-aikar da ya aikata kawai na ke ji, inji Adam.

Adam bai da]e a garin Jos ba sai kawunsa ya sa shi makaranta. A Turance, ya ce mana, "I was enrolled in Islamiyya primary school. When I finished, I was later admitted at Government Secondary School, Laranto." wato yana nufin ya yi karatun Islamiyya, da ya gama aka saka shi a makarantar Sakandaren Gwamnati ta Laranto.. Kun san a industiri akwai magulmata masu cewa wai Adam Bakatafe ne, ya saje da Hausawa yana yin fim. Har ma wasu na cewa ba su san ma’anar ‘A’ ]in nan ta tsakanin sunansa ba.

Da aka yi masa tambaya kan ha}i}anin gaskiyar salsalar sa, sai Adam ya gyara zama ya ce, "To yau dai tun da an tambaye ni, bari in fa]a ga duk wanda ya damu ya sani ko ya ji. Ni dai Bahaushe ne cikakke, ba Bakatafe ba."

Ya ci gaba da cewa, "Da farko, kakana zuwa Zangon Kataf ya yi, daga shi kuma mahaifina ya ha]u da mahaifiya ta ne a Saminaka, suka yi aure, suka dawo Zangon Kataf da zama, inda aka haife ni."

Adam ya }ara bin tushensa inda ya ala}anta kansa da jinin Larabawan Shuwa. "Kai, ni fa akwai jinin Shuwa Arab a jiki na, domin mahiifiya ta tana da jinin Shuwa Arab ajikinta".

A halin yanzu Adam ya dawo da mahaifiyarsa Kano inda ita ma take ]an]ana romon ribar industiri. "Ni ban ga dalilin da zai sa in bar mahaifiya ta can nesa ba, na fi so in matso da ita kusa da ni. Kuma na gode Allah da azurtawar da a yi min. don haka wajibi na ne in kyautata wa mahaifiya ta."

To mu ci gaba. Da yake Adam (komu ce Adamu) bai yi nufin ci gaba da karatu ba, yana kammala karatun sakandare a Laranto, sai ya tarkato kayansa ya nufo Kano, kaitsaye ya zarce gidan buga wa}o in fina-finai na ‘Lenscope Media’ mallakar furodusa/darakta Sani Mu’azu, wanda shi ma ]an Jos ne.

"Shekara biyu na yi ina cin ba}ar wahala a ‘Lenscope Media’ inji Adam. "Haka nake zaune ina kallon kaina a matsayin jarumi, amma har zuci na san ni ba jarumin ba ne, saboda idan na yi sin ]aya, ban san ranar sake yin wani ba."

Yana cikin irin wannan zama ne sai sakatariyar kamfanin Lenscope ]in, mai suna Hauwa M.D. (Kun tuna ta?) Ta fara tausaya masa ganin cewa matashin ]an fim ]in yana cikin halin rayuwar na ware-ga-dangi. Sai ta ba shi shawarar me zai hana ya koyi yadda ake ki]a, wato buga wa}a.

Da farko Adam bai ]auki shawarar ba, sai ya nuna mata cewa, "Ni fa na zo Kano ne don in zama jarumi in yi fim, ba in buga wa}a ba."

Amma da ya ga uwar bari, kullum mafarkin zaman sa jarumi na }ara faskara, sai ya nemi fitaccen maka]in nan Ibrahim Danko ya ri}a koya masa yadda ake buga wa}ar a Lenscope ]in. "Gaskiyar magana ka ji yadda aka yi na zama maka]i ba a son raina ba."

Cikin }an}anen lokaci aka san Adam A. Zango a matsayin maka]i, domin ya buga wa}o}in fina-finai masu yawan gaske.

Shin ya ya aka yi bayan ya zama mashahurin maka]i kuma ya riki]e ya zama fitaccen jarumi?

Ya ba mu labarin: "To da na tara ku]in da zan iya yin fim, sai na yi tunanin in yi fim nawa kuma in zama jarumin fim ]in nawa tunda matsayin jarumi."

Da wannan ne ya yi fim ]in sa na farko a matsayin jarumi mai suna ‘Surfani.’

Adam ya yi suna a fina-finan soyayya, musamman fim ]in sa ‘Raga, wanda a yanzu ake kiran sa da suna fim ]in, wato Mai Raga. Amma ‘Zabari,’ Kallabi’ da irin su ‘Kawanya’ ne suka fara fito da shi. Wannan tashe da ya yi kuwa ya sa Adam ya yi wa matasa masu buga rol na soyayya zarra. Ko a gida ko a lokeshin ko a fim, inda Adam yake za a gan shi ‘yan kallo suna baibaye shi. Ofishinsa na buga wa}a mai suna ‘Crown Studio’ kuwa wata matattara ce ta matasa maza da mata. Sai dai kuma duk da wannan, shi Adam muradinsa tun farko shi ne ya zama wani tantirin ma}etaci, ]an daba, bos, irin su Shu’aibu Kumurci.

To ya ya aka yi ya zama jarumin soyayya?

Ya ce, "Gaskiya Ali Nuhu ne zan iya ce malamina. Shi ya koya min yadda ake yin rol na soyayya. Kai, sai da ta kai Ali kan zaunar da ni yana koya min yadda zan ri}a yin kukan jimamin soyayya a fim. To yanzu ga shi ina jin da]in wannan rol ]in, don ya kar~e ni."

Shin Adam yana sane da yadda ‘yan mata ke yi masa son daga-nesa-nesa kuma masu yawan bugo masa waya fa?

Sai ya amsa da cewa, "Ai ina sane, mahaifiyata ce ke ce min in ri}a yin kaffa-kaffa da ‘yan matan zamani. Shi ya sa ma take ta bi na da lallami cewa in yi aure kawai ko sa shafa min lafiya."

To Adam A. Zango muna jiran mu ga wannan rana ta aurenka. Haka su ma ‘yan matan naka, suna jira.


TARE DA SAIISU NA UKU

RABILU MUSA IBRO SARKIN BARKWNCIN WASAN HAUSA
DAN IBRO YA KUMA SIYASA TSUNDUM HAR WUYA, KOKARINSA SUN KAFA GWAMNATI A KANO


Dan mi a cikin camamar da kake yi anfi nuno ka a matsayin mayaudari, wanda ke yin yaudara daga karshe ya samu ya tsira ?

E’ amma kuma idan ka kula ni ba hali na bane, tun da za ka ga ai a wasa ne, amma kuma in ka zo ka same ni, sai ka gan ni shiru-shiru, to ai muna fadakarwa ne saboda akwai masu irin wadannan halayen.

Mun lura a cikin fina-finan ka wani sa’in ka kan zolayi wani mutum da baya cikin wasar koma ka zage shi, wannan yana nufin ba ka shiri da shi ne ?

In dai ka ji na tsokano wani dan sentimental, kama daga darakto har zuwa yan wasa, to duk haraka ce ta wasa amma ba dan wani rishin jituwa ba, kamar yadda naji wani dan kallon wasa yana tambayata ko mine ne tsakanina da Ali Nuhu ? tsakani na da Ali Nuhu ba wani abu sai zaman lafiya, dan ko anan in dai zan ji wani abu na cin mutuncin Ali Nuhu, to ina mai tabbatar maka sai inda karfina ya tsaya, tunda ni ba wani abun bacin rai da Ali Nuhu ya yi man, kuma shi ma ba abunda na yi masa sai zaman lafiya.

Ana rade-radin cewa Ibro ya taba furtawa da bakin sa zai auri tsigai saboda shakuwa da kuka yi da juna mine ne gaskiyar zancen ?

Ba gaskiya bane, ni banga wani abun shawa a jikin Tsigai ba balantana in aure ta, ba kuma auren ne babu a tsakani na da ita ba, kawai saboda shakuwa da dadewa shi ne yasa duk wadannan abubuwa suka kau a tsakanin mu.

Mi yasa a shekarun da suka gabata an sha gayyatar ka, domin ka yi wasa a birnin Yamai amma baka zo ba, miye dalili ?

Kasan yanayin aikin namu, a kulum akwai abubuwan da zamu yi, dan haka dole ne wani sa’in sai an karya wasu alkawura kafin a cika wasu, kamar yanzu zuwan da nayi a nan Nijar,akwai alkawura da dama da na karya, ka gani suma ba za su ji dadi ba, amma yanzu in muka koma doli suma mu yi kokarin faranta masu.

Ana cewa kana nuna kishi a kan masu kwaikwayon wasanka na dan Ibro, mine ne gaskiyar lamarin ?

To ai ni murna ma nake yi, ba wai sai a nan Nijar ba, ko a can Nijeriya duk garin da ka je sai ka samu Ibro, to amma duk abinda suka yi ko yaba masu kallon su dariya, sai kaji sun ce da dai Ibron ne da abin ya fi haka, ko kuma sai yayi kaza, to kaga dolin dai ni Ibron na gaskiya a ke tunawa ba kai mai kwaikwayon Ibron ba.

Wane kira gareka dangane da hadin kan yan wasan kwaikwayo ?

Dan wasan kwaikwayo ai bashi da hadin kai, yanzu misali ka dauki kafa daga nan Nijar ka je Najeriya kace kana son ganin dan Ibro, in ka hadu da wani dan wasan kwaikwayon nuna ma zai yi ni ba mai sauraren jama’a bane, ko kuma ya nuna ma bana garin, ko kuma in kaje ma bazan saurare ka ba, sai kuma ya san yadda zai sa ku dai daita da shi, to illar dan wasan kwaikwayo kenan, amma ni abida nike gani irin wadannan ba su bi iyayensu ba, basu kuma san darajar iyayensu ba, balantana su san darajar wani, amma in dai kai dan wasan kwaikwayo ne, ka sa Allah a zuciyar ka, ba ka tunanin yiwa wani mugunta, mu fa tuna duk wanda ya yiwa wani mugunta, ba wancan ka yiwa ba kanka ka yiwa, kuma ba inda zaka je.

Ai ga irinta nan, wani dan wasan na nan kulum yana yawo da riga daya, wani kuma tun a wannan Sentimental din da aka aro wasu rigunan har yanzu yaki ya cire a mayarwa mai kaya abinsa, ka gani duk irin wadannan mutane muna tare dasu

A karkashin tsarin shara’ar musulunci a jahar kano, wasu Malaman addinin Musulumci na gani wasannin ku fitsara ne bai dace da shara’a ba, ko mi zaka ce a nan ?

To shi shugaban gwamnatin ma, Malam Ibrahim Shekarau burinsa har kulum shine, ya za’a yi a jawo yan wasan kwaikwayon domin su dada yada addinin musulumci, saboda shi kansa Malam Ibrahim Shekarau ya san cewar mu yan wasan kwaikwayo mun fi wasu masu wa’azi, tunda babu wanda zai je yayi wa’azi ya tashi bai zagi wani ba, mu ko yan wasan kwaikwayo nunawa zamu yi " Ra’ayil Aini " ga yadda abin yake marar kyau ,ga kuma yadda abu mai kyau yake, a saboda haka mu yan wasan kwaikwayo munfi masu wa’azin da za kaga sun buda littafi sun jawo ayar Alkur’ani ana maganar Allah, amma sai ka ji an zagi wani, shi ko Annabi Mahamadu S.A.W har ya gama wa’azinsa ba ka ji ya zagi wani ba, balantana ya takurawa wani, to dan haka suma Malaman ya kamata su tsaya su gyara, su yi koyi da shugaban mu Annabi Mahamadu S.A.W mai makon in suka ga mun yi abinda ba daidai ba su yi wa’azi a tsanake a’a basa yi, kai wani sa’in ko abun dai dai ne, dan dai mutum ya samu wani abu sai ka ji yana ta zagi yana ta suka, dan kawai a kirawo sa a dan yafuta masa wani abu, kuma ana yafuta masa sai ka ji ya dena magana, kai ni akwai wani malami gaba daya ma cewa yayi ni kafiri ne, to yanzu ni ina son ya janye kalmar kafirci a kaina, nace

" La ilaha illal-Lahu Mahamadar Rasulul-Lah Sallalahu Alaihi Wasallam " amma ni abinda na zata ta yiyu shi mai ce mani ni kafiri ne, babarsa ce ta mutu a wani hali na asha, ya ke son shima ya kafurta wani, kuma su malaman da kansu ke fadin cewa duk wanda ya kafurta wanda ba kafuri ba kansa ya kafurta, ni dai kira na ga irin wadannan malamai idan sunga munyi wani abu da ba dai dai ba, to su kirawo mu su gyara mana, ko su ce mana ga yadda ya kamata mu yi mu gyara, wannan shi ne kiran da nike yi masu.

Ra’ayi mun gode !YAR BUZUWA NIGER
KIMA YANBIRNI
wata shararriyar kungiya wadda ya cire tuta awajan shirya finafinan hausa abirnin Maradi, wannan karinma sun shirya wani shararren Albam wanda suka yiwa suna YAR BUZUWA, wand zai fito nan badajimawaba cikin wannan sabuwar shekara ta 2010 domin neman karin bayani sai a nemi su akan wannan adreshi: kimayambirni@gmail.com, +22796721606,+22794300195
Daga Salisu Nauku (cica)


KARAGA
DAUKAR NAUYI BINIYA TAKO TAKO
GARGADI
Ba a yarda wani ko wasu su canja wannan labari zuwa wata siga ba, yin hakan kuskurene, dan haka sai akiyaye


GABTARWA
Anyi wani Sarki a wani gari wanda ya kasance mai adalci ga al’ummarsa yana kma kyautata masu mutuka, da sanin dara jar nagaba dashi, sannan kuma ga san addini .
Saidai kuma wazirin sa zuciyarsa cike take da babakere, da san abin duniya, ana nan sai Sarki yabada umarnin duk wani wanda ya boye kayan abinci domin suyi tsada toya fito dasu, domin kuwa shi Sarkin ya sauwake farashi. Tuni waziri yashiga tunanin mafita domin kuwa yanadaya daga cikin manyan masu fasa kwaurin kayan abinci .
Bayan shawarar da Sarkin gida ya bashi a matsayinsa na babban aminin sa, sai suka nufi wajan wani mashahurin Boka, inda yabasu shawarar Waziri yasa dansa yanemi auran yar’ Sarki idan yaaure ta sai akashe Sarkin, Sarautar kuma ta koma gidan Waziri
Amma inaa bukatar bata biyaba saboda ita Gimbiya akwai wanda takeso wani dan Fulani Makiyayi, wanda yasa suka kasa biyan janyo rashin biyan bukatarsu ………………………….


FITA TA DAYA
(daji dan Fulani da shanu)
Dan fulani da shanu, sunayin kiwo, yana kula dasu
(waje cikin daji da rana)

FITA TA BIYU
(kauye cikin gida)
Ya dawo daga kiwo, yazo wajan mahaifiyarsa tana dakan fura, suka gaisa tace masa sannun da zuwa tace ya shiga daki ya sha fura ya huta .
(waje cikin tsakar gida )

FITA TA UKU (kauye cikin gida )
Babansa ya fito daga daki da goran ruwa, yace jauro, da karfi shi kuma yana turken awaki, ya amsa ya tahu da gudo yace wa masa baffa gani, shi kuma yace masa idan kagama abin da kake kaje ka kai shanu rafi, ya amsa cikin ladabi.
(waje tsakar gida da rana)

FITA TA HUDU ( kauye a daji)
Jauro ya hadu da abokinsa yadawo daga guna, sannan kuma suka gais aya tambayeshi kwana biyu, shi kuma yace yana nan lafiya ayyukane sukayi masa a gona, sannan suka alkawarin zasu wajan wasan sallah sanar sallah.
(waje daji da rana )

RANAR SALLAH
FITA TA BIYAR( cikin wajan wasan sallah)
Jauro da abokinsa suna ta zagaya wajan sanni , yammata da samari kuwa sai sha’anin gabansa yakeyi (cut).
Wadansu masu wasan gargajiya suna ta wasansu Gimbiya kuma tazo wajan wasan sallah tana kallo ita da kuyanginta(cut)
Su jauro kuma suka zo wajan suna kallo wasan. Kuma suna yaba n kyan gimbiya.
(wajan wasan sallah)

FITA TA SHIDA ( kauye cikin gida)
Jauro ne shi da babansa suna hira kuma akan yadda aka shirya wasan sallah, mai kayatarwa, shi kuma uban ya bashi labarin sarki da kirkinsa, daga lokacin sallah yayi suka tashi suka tashi domin suyi sallah.
(tsakar gida da rana)


FITA TA BAKWAI( Fada)
Fada ta cika ana jiran zuwan sarki, daga nan sarki shigo fada kuwa ya mike domin girgimamawa, bayan ya zauna sannan kuwa ya zauna, bayan ya zauna yan majalisar sarki kuwa yazo yayi gaisuwa, sannan sarki yayiwa yan majalisarsa barka da sallah, kuma yayi musu bayani akan aji tsoran allah wajan al’amuran yauda kullum, ya kuma bada sanaewa ya bada wata guda duk wanda ya boye kayan abin abinci dan suyi tsada ya sayar tu ya fito dasu , domin talakawa su sami abin sawa abaki. Daga nan sarki yayi sallama ya kuma gida.
(cikin fada da safe)

FITA TA TAKWAS( gidan sarki)
Waziri ne shi da sarkin gida, suna tataunawa akan abin dasarki ya bada umrni bayan anfito daga fada, waziri yace gashi yanzo nafi kuwa aje abinci domin gaba, amma ga wannan doka, shi kuma sarkin gida yace ai ranka ya dade ya kamata mu dauki mataki akan wannan abu, waziri kuma yakara saba babbar rigarsa yace ai baikamata muyi magana ananba kasameni agida yau dadare.
(harabar gidan sarki)

FITA TA TARA (gidan sarki)
Sarki ne kishingide yana karatun a’lkurani, jakadiya tayi sallama rike da tire dauke da kayan marmari ta aje bayan tayi gaisuwa harzata fita, sarki yace yana san ganin Gimbiya tace to(cut)
Gimbiya ta shigu tayi gaisuwa, sarki yayi mata nasiha akan rayuwa, ya kuma ce tayi riku da addinin tad a a’ladun Bahaushe.
(wajan hutawar sarki)

FITA TA GOMA (gidan waziri)
Waziri ne shi kadai, sai zirga zirga yakeyi shika dai (cut)
Sarkin gida ya shigo, bayan sun gaisa waziri yace tundazo yake jiran sa domin su tattauna akan maganar nan, can sai sarkin gida yace ai akwai mafita, yace masa meye mafita, shi kuma yace masa Boka zaiyaul zaaman gaskiya ne kayi gakiya, dama ni wannan abun ya isheni, yanzo gani nine waziri amma na zama kamar hoto baa shawartata akan kumai Borin ma da wasan yan’daudun baayi, shi kuma sarkin gida yace ranka yadadi ai sarautarma asali ta gidanku ne, kamata yayi mudau mataki, to ni zan tafi gida sai goben zanzo muje wajan Bokan.
(gidan waziri da dare)

FITA TA SHA DAYA (gidan sarkin )
Gimbiya Hafsat ce ita da mahaifiyar suna hira Hajiya Binta, tana mata wasa da kai, ita kuma cikin shagwaba suke hirar tasu, Hjiya ta tambayeta tana da wanda take so domin kuwa mai martaba yace in tabayeki, ita kuma tace gaskiya har yanzo bawani take so, kuma ita bata san auran dan wani sarki ko dan attajiri, uwar tace to balaifi tashi kije kiyi sallah lokaci yayi, tace to mama yaufa zan fita Lanbo da yamma, uwar tace ba kumai.
(gidan sarki dafe)

`FITA TA GOMA SHA BIYU (Lambo)
Gimbiya ce ita da kuyanginta suna hira da wasanni, suna tayata nisahdi (cut)
Can sukaji karar sarewa daga wani bangari, hankalin su yayi wajan, gimbiya ta mike tsaye ta nufi wajan da sarewa take (cut)
Suka sameshi shi kadai yana busa, ya tsaya yana kallonsu har suka karasu wajansa, ya tsugunna ya gaida ta, taamsa cike da kollonsa kallo na soyayya, ta tambayesa meya kawushi nan yace shi makiyayi ne ya shigu nan dan yahuta, shanun nasa kuma suna wajan abokin sa yana tayashi kiwo, daga ta bukaci cewa tanasan ganin sa gobe , sukayi sallama.
(cikin Lambo da yamma)

FITA TA SHA UKU (cikin daji)
Waziri ne shida sarkin gida suna tafiya cikin daji, sun nufi wajan Boka (cut)
Suka same shi akan iska, bayan sun gaya masa bukataun su, Boka ya ce idan waziri yana san zama sarki sai dai tura dansa ya nemi auran gimbiya, idan yaaureta shi kuma zai bau wani magani asawa sarki a abinci, idan sarki ya mutu sarauta ta dawo gidan waziri kenan .
Daga nan suka yi sallama da boka, suka tafi.
(daji wajan boka da yamma)

FITA TA GOMA SHA HUDU (cikin Lanbu)
Gimbiya na zaune ita kadai tana jiaran jauro, ga kayan marmari amma takasa sha, ta kuma gagu, can sai taganshi ya shigo, yayi gaisuwa sannan kuma suka yi hira akan soyayya, da farko yaki amin cewa, amma daga bisani ya amince dacewar bazai iya zuwa gidansuba.
(cikin lambu da yamma)

FITA TA GOMA SHA BIYAR (Fada)
Sarki yayi jawabi, bayan fada ta cika, sannan yayi bayani akan rikan addini da Alamuran yau da kullun, wajan harkokin su, sarkin gida kuma da waziri sai kallon juna suke a mufunce.
(cikin fada da safe)FATATA GOMA SHA SHIDA (gidan waziri)
Waziri ne yake yiwa dansa jawabi akan yaje gidan mai martaba ya na san gimbiya, idan kuma yayi hakan za adaura masu aure cikn kankanin lukaci, shi kuma ya amince akan hakan, yana mai tunanin gashi nan ya zama sarki (cut)
Daga bangaran gidan sarki kuma gimbiya ce ita da mahaifiyar ta, tana ce mata yanzu tasami saurayi wani dan fulani (cut)
Mahmud yace ya amince zai jarraba.
(cikin gidan waziri dasfe)

FITA TA GOMA SHA BAKWAI (gidan sarki)
Sarki ne zaune shi kadai yana karatun kur’ani, jakadiya kuma ta shigo da kayan marmari, da zata fita sai ya umarceta data kira masa gimbiya Hafsat, bayan ta shigo yayi mata nasiha akan ta kula da addini, da kunakula da aladun gargajiyar mu, daga nan kuma yata ta tashi ta tafi.
(gidan sarki wajan hutawa)


FITA TA GOMA TAKWAS ( gidan sarki)
Sarkin gida ne tare da sarki yana masa hirar yakamata ahada dan wajan waziri da gimbiya aure saboda bisa laakari da hankalin yaron, sarki yayi farin cikin hakan sosai, yace ai wannan ba damuwa indai yaran sun hada kansu to ai sai ayi, daga nan yayi sallama dasarki ya fita. (gidan sarki wajan hutawarsa da rana)

FITA TA GOMA SHA TARA (gidan sarki wajan gimbiya)
Mahmud ne dan waziri shida gimbiya, yana bayyaan mata manufarsa tasan auran ta, ita kuma takio amincewa dashi tace tu ni tana da wanda take so, wani dan Fulani ne kuma yaka mata yaje yayi masa barka domin ta zabe shi a matsayin weanda zata aura.
Ya fita fusace ,yabarta anan zaune, yana ta fada wai ya zaayi ta rasa wanda zata so, saiwani talaka.
(gidan sarki wajan hutawar gimbiya da yamma)
FITA TA AHIRIN (kauye )
Jauro ne shida mahaifiyarsa suna hira akan maganar gimbiya,
(da rana )

FITA TA ASHIRIN DA DAYA
Sarkin gida ne shida waziri suna tattauna yadda gimbiya taki amincewa da dan waziri.
(da dare)


FITA TA ASHIRIN DA BIYU (fada)
Sarkin gida ne yake fadar dokar aurar da yar sarki, idan kuma taki amincewa kuma sai dai taje dandali bisa aladar garin, sauran fadawa kuma suka amince da hakan.
(cikin fada dasafe)

FITA TA ASHIRIN DA UKU (gidan sarki)
Gimbiyace take tunanin gobe zata dandali wazan azabar miji, saboda haka ita bazata zabi mahmud ba dan fulani zata zaba, kuma zata aika masa kas ayakirata da gimbiya.

FITA TA ASHIRIN DA HUDU (cikin gri)
Mutan gari ne suke tattauna zuwan gimbiya dandali.

FITA TA ASHIRIN DA BIYAR (cikin gari)
Mutan gari ne suke tattauna zuwan gimbiya dandali.

FITA TA ASHIRIN DA SHIDA (dandali)
Wajan wasan dandali ya cika, domin kuwa gimbiya zata zabi miji.

FITA TA ASHIIRIN DA BAKWAI(Gidan waziri)
Waziri da sarkin fada sunyi mutukar bakin cikin rashin zaben Mahmud dan waziri, amma sun sake dabara.

FITA TA ASHIRIN DA TAKWAS (kauye)
Waziri ya turo fadawansa su cima dan fulani Mutunci.

FITA TA ASHIRIN DA TARA(gidan waziria)
Mahmud ne shi da abokin sa suna tattauna matsalar rashin zabensa da gimbiya batayiba.

FITA TA TALATIN (gidan waziri)
Waziri ne shi da jakadiya, yana neman amincewarta ta yarda tasawa sarki magani a abinci.
FITA TA TALATIN DA DAYA
Jakadiya ce take sa magani acikin abincin sarki shikuma ya isketa

FITA TA TALATI N DA BIYU (gidan sarki )
Sarki ne yake gimbiya da jauro nasiha domin kuwa gobe za a daura musu aure.
karshe
ALHAMDULILLAH
DAGA TASKAR SALISU NA UKU
TUNANINA AKAN AKAN MAAUNIN DUBA FINA FINAI
Gaskiya ne hukumar tace finafinai ta jihar kano tayi iyakacin kokarinta wajan fito da maaunin doba finafinan hausa, inda ta kalli fuskokin wasu abubuwa kamarsu Addini, Al’ada, Siyasa, da mutuncin dan Adam wajan kirkiro dokokin daza ayi amfani dasu wajan auna ingancin wasan hausa kafin ya fita kasuwa, to amma a tunanina duk da cewa baizama lallal duk masu shirya finafinan su kasance hausawaba, ku kuma zata iya yiyuwa mahaushe ne ammam bashi da addini ku kuma bahaushe amma kirista, to amma kuma yayi fin, kuma wanda yake dauke da sako mai ma’ana amma kuma yasa addininsa ko kuma Al’adarsa, ni ina ganin yakamata suma a fito musu da maauninsu domin tantance finafinansu.
Wasan hausa ya kasu a kalla kashi hudu kamarsu Camama wato barkwanci, santimental wato na birrni, adventure na tarihi kenan, da kuma na camama sentimental maana wanda zaa fara a kauye a gama a birni, to ni a tunanina yakamata a babbance fuskukin da za a auna kuwanne fim, misali fim din camama zakaga yana kamanta zamantakewar bahaushe a karkara, to amma yadda wasu suke shirya finafinan sai kaga sun canza wadansu abubauwa na bahushe, a nawa tunanin ai bakuwanne bahaushene mai barkwanciba, amma sai kaga gaba dayan mutanen da suka fito a wani fim har agama duk barkwanci suke, wanda ni kuma inaga bahaushe akwi jarumta, hankali, hikima, fasaha, ilimi, ladabi da tarbiya a duk al’amuransa, amma kuma da dama daga cilki masu shirya finafinan camama suna barin irin wadannan abubawa, kaga kuwa akwai bukatar a kalli wannan al’amari da idon basira, domin kuwa duk wanda ba bahusheba idan yana kallon iri wadannan finafinai kawai zaidinga yi bahushen mu nakauye wawa wawa, yakata yan’ uwana Directocin camama su ringa kyautata labaransu.
Idan mun kalli maaunnin da hukuma tatanada akan tace wasan hausa, zamuga ta kawu wadansu abubauwa wadanda sun fiyin tasiri akan finafinan birni wato sentimental, kuma ni inaga finafinai natarihi wato adventure, kuma muma anan kasar hausa muna irin wadannan labarai misali irinsu tarihin kasar hausa musamman na Barbushe da tsunburbura wadanda sukayi zama a kano a doshen dala, domin kuwa idan tarihi ya nuna mana cewa matanen wancan lokacin suna zuwa wajan bautarsu ta karshen shekara ajindir domin jin labrin shekara a wajan Barbushe wanda shine wakilin tsunburbura a wancan lokacin, to kaga akwai bukatar atanadi irin yadda za a maida wannan labari zuwaga fim, sannan kuma idan ka kalli tarihin sarakunan mu nada ba irin wannan mulkin suke gudanarwaba akwai bautar wadansu abubuwa, kuma a yanzo nan an fara irin wadannan finafinai domin akwai wani fim mai suna NASARUN MINALLAH na wani Directa wanda ke katsina mai suna Usman U N M wanda ya kunshi yadda ake dautar gumaka, da wuta dasauran abubawa
Zanci gaba daga Naku SALISU ABUBAKAR (NA UKU)

No comments:

Post a Comment